INTRO:
Yesu Kristi, yayi kusan zuwa--- zaya zo ba tsamani--- ko da safe, ko da rana, ko da yamma bamu sani ba, mu yi zamanmu da tsaro-oh-
Chorus:
Babu wanda ya sani randa Yesu Kristi zai zo.
Adlips: (Babu wanda ya sani--e-- mu yi zamanmu da tsaromu zauna a shirye,)
Stanza 1:
Ko ka sani ne, ko kin sani eh, ko kun sani randa Yesu Kristi zai zo,
Allah ya baka baiwa, baiwa ka yi aiki da shi ka dauki wannan baiwa, kana ta bin duniya,
Allah ya baki baiwa, baiwa ki yi aiki da shi kin dauki wannan baiwa, kina ta karwanci,
Randa Yesu zai zo, zai tambayeku, wannan baiwan da na baku menene kun yi da shi.
Adlips: Bamu sani ba, ko da safe ne, ko da rana ne, uwo.
Stanza 2:
Randa Yesu zai zo, zai tambayeka,
wannan baiwan da na baka ka yi shi ko baka yi.
Randa Yesu zai zo, zai tambayeki,
wannan baiwan da na baki, kin yi ko kin bata lokoci yar'uwata.
Adlips: Bamu sani ba, mu yi zaman shiri, don bamu sani ba-a-a- uye eh
Bridge:
Babu wanda ya sani, randa Yesu zai zo,
Babu wanda ya sani, ranan zuwan mai ceto-o-
Babu wanda ya sani, randa Yesu zai zo, to mu yi zamanmu da shiri,
mu shirya a ko yaushe---
Stanza 3:
Ko ka sani ne, ko kin sani eh,
ko kun sani randa Yesu Kristi zai zo,
Babu wanda ya sani a duniya randa Yesu zaya zo-o- to mu yi zamanmu da shiri,
mu shirya a ko yaushe,
Ko da safe, ko da rana, babu wanda ya sani,
Ko da yamma, ko da dare, babu wanda ya sani,
ko ka sani ne, ko kin sani eh, ko kun sani ni kam gaskiya ban Sani ba